Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Sanata Abubakar Kyari a gidansa da ke Abuja.
Sanata Kyari, wanda ya bayyana goyon bayansa ga Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu wanda ya cancanci mukamin shugaban jam’iyyar APC na kasa sama da Ganduje.
Sanata Kyari ya taya Dakta Abdullahi Umar Ganduje murna, inda ya yi addu’ar Allah ya taya shi riko.
Mataimakin sakataren kudi na jam’iyyar APC na kasa, Hon. Dattuwa Ali Kumo, yana daga cikin wadanda suka ziyarci Ganduje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp