A yau Juma’a ne ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya kira taro, domin nazari da tantance yanayin ayyukan raya tattalin arzikin kasa na shekarar 2024, da tsara salon tafiyar da jam’iyya, da ayyukan yaki da cin hanci, da nazarin dokokin hukunta laifuka na jam’iyyar. Taron na yau ya gudana ne karkashin jagorancin shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping.
Yayin taron, an amince cewa tattalin arzikin kasar Sin ya yi nasarar farfadowa a bana. Kaza lika zaman ya jaddada muhimmancin aiwatar da managartan matakan zaburar da tattalin arziki, da kandagarki da dakile hadurra, da kyautata kwarin gwiwar al’umma, da karfafawa da kyautata saurin farfadowar tattalin arzikin kasa, karkashin ayyukan raya fannin na shekarar 2024.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Raba Tallafi Ga Masu Kananan Masana’antu
- Kamata Ya Yi Kasashe Masu Ci Gaba Sun Cika Alkawarin Da Suka Yi Na Samar Da Kudaden Taimakawa Kasashe Masu Tasowa Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi
Har ila yau, zaman ya yi kira da a kara azamar samar da ci gaba, yayin da ake tabbatar da daidaito, da karfafa daidaito ta hanyar samar da ci gaba, da kafa sabon tsari kafin rushe tsarin raya tattalin arzikin kasa da ake kai a shekarar dake tafe.
Bugu da kari, an dorawa sassan ladaftarwa da sanya ido, alhakin ingiza matakai cikakku, kuma masu inganci, wadanda jam’iyya za ta aiwatar domin jagorancin kan ta, da yin aiki tukuru don inganta yanayin da’a, da karfafa bin doka, da yaki da cin hanci. (Saminu Alhassan)