Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya caccaki tsofaffin shugabannin Arewa bisa gazawarsu wajen magance talauci, gibin ababen more rayuwa, da samar da hadin kai a yankin duk da rike manyan mukamai a gwamnati.
Da yake magana a taron tattaunawa kan ci gaban matasan Arewa, wanda cibiyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna, Gwamna Sani ya gargadi cewa idan Arewa ba ta gaggauta daukar mataki kan matsalar tsaro da ci gaban yankin ba, “mutanen Arewa ba za su iya kwana a gidajensu ba nan da shekaru biyar.”
- Rahoto: Yanayin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Kasar Sin Na Ci Gaba Da Habaka
- Matatar Dangote Ta Fara Fitar Man Fetur Dinta Zuwa Kasashen Afrika
Ya yi kira ga shugabanni da su kirkiro wani tsari na musamman don bunkasa matasa tare da hadin gwiwar duk masu ruwa da tsaki.
Ya ce, “Dole ne mu yarda cewa mun gaza taimakon mutanenmu. Zargin wasu ba zai warware matsalolinmu ba.”
Gwamnan ya nuna damuwa kan koma bayan yankin duk da dumbin kudaden da aka kashe, yana mai cewa matsalar tsaro, kamar ta’addanci da ‘yan bindiga, ta lalata al’ummomin Arewa.
“Matasanmu sun fi shan wahala, kuma mun kasa magance tushen matsalolin,” in ji shi.
Sani ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa, inda ya ce, “Mutanenmu suna neman amsa, kuma dole mu ba su.”