Shugabannin kasashen duniya, da jagororin kungiyoyin kasa da kasa, sun bayyana baje kolin CIIE dake gudana yanzu haka a birnin Shanghai na kasar Sin, a matsayin muhimmin dandalin kasa da kasa, na bunkasa cinikayya da zuba jari, da hadin gwiwar sassan duniya.
Shugabannin sun kuma jinjinawa Sin, bisa muhimmiyar gudummawar da take bayarwa, ga farfadowar tattalin arzikin duniya.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Ghazouani, ya ce bikin baje kolin CIIE ya riga ya zamo daya daga muhimman dandalolin kasa da kasa, dake baiwa kasashen duniya, da kamfanoni damar baje hajojin su, tare da gano sabbin damammaki na cinikayya da zuba jari, da zurfafa ci gaban hadin gwiwa, da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya.
Game da hakan, shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, ya ce, yana da karfin gwiwa game da nasarar hadin gwiwar tattalin arziki da kasar Sin. Ya ce bikin baje kolin CIIE, babban dandali ne na bunkasa damammakin zuba jari da gina alakar kasuwanci.
Ita kuwa babbar daraktar asusun ba da lamuni na IMF Kristalina Georgieva, cewa ta yi duniya na bukatar karin hadin gwiwar kasa da kasa, kuma hakan ne ya sa baje kolin CIIE, da sauran makamantan sa ke da muhimmanci, wajen samar da damar cudanya da tattaunawa.(Saminu)