• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Duniya Za Su Gudanar Da Taron Sanya Hannun Jarin Bunƙasa Ƙudurorin Muradun Ƙarni A Sifaniya

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
5 months ago
Duniya

A cikin wannan watan ne na Yuni, 2025, shugabannin kasashe daba-daban na duniya za su hallara a birnin Sevilla ta kasar Sifaniya a wani yunkuri na ceto domin gyara yadda duniya za ta sanya hannun jari a tsarin ci gaba mai dorewa.

Shekaru goma bayan amincewa da tsarin manufofin ci gaba mai dorewa da kuma alƙawuran da duniyar ta dauka domin cikawa, kashi biyu cikin uku na abubuwan da aka alkawarta, ba su samu ba, kasashen duniya na samun gibi na kimanin Dala triliyan hudu a kowace shekara daga kasashen da ke bayar da tallafinsu ga shirin domin sauke nauyin wadannan alkawura kafin 2030.

  • Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Albarkacin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” Karo Na Farko Na MDD
  • Atalanta Na Neman Yuro Miliyan 50 Daga Duk Kungiyar Da Ke Son Daukar Lookman

A halin yanzu dai, tattalin arzikin duniya na yin kasa, ana samun karuwar tashe-tashen hankula ta fuskar kasuwanci, ana samun raguwar kasafin kudi ta fuskar bayar da agaji yayin da ake kara kashe kudaden ta fannin tsaro da aikin soji. Yawancin tallafin da ke fitowa daga wasu kasashe na duniya ya shiga wani hali na tabarbarewa da ba’a taba ganin irin sa ba.

Rikicin dake dakile ci gaban duniya a fili yake amma yana tasirantuwa ne a cikin talakawa masu kwana da yunwa, da yaran da ba sa samun riga-kafi, tilasta wa ’yan mata barin makaranta da kuma al’ummomin da aka hana su ayyukansu na yau-da-kullum.

Ya zama dole mu gyara hanyar, kuma hakan zai fara ne a taron kasa-da-kasa karo na hudu kan samar da kudade don ci gaba a Sevilla, yayin gudanar da wani shiri na nuna kishin kasa, da tallafi na duniya, kuma ya kamata a yi amfani da shi domin sanya hannun jari a cikin manufofin ci gaba mai dorewa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Shirin dai zai kunshi abubuwa masu mahimmanci guda uku;

Na farko, Taron Sevilla zai taimaka wajen zaburar da shigowar tallafi zuwa ga kasashen da suka fi bukatarsa.

Na biyu, dole ne kasashe su kasance a kan kujerar tattara albarkatun cikin gida ta hanyar karfafa samar da kudaden shiga da magance rashin biyan haraji, hadin gwiwar kasa da kasa. Wannan zai samar da albarkatun da ake bukata sosai domin bayar da fifikon kashe kudade a wuraren da ke da tasiri mafi girma kamar ilimi, kiwon lafiya, ayyuka, kariya ga zamantakewa, samar da abinci, da makamashi irin na zamani.

A bangare daya kuma, akwai bukatar bankunan ci gaban kasa, da na shiyya-shiyya da kuma bankunan raya kasa-da-kasa, su hada hannu domin saka manyan jari.

Domin tallafa wa wannan shirin bayar da lamuni na wadannan bankunan, akwai bukatar a ninkawa sau uku ta yadda kasashe masu tasowa za su iya samun babban jari ba tare da an dora masu ruwa mai yawa ba.

Hakan zai bayar da damar ajiyar dukiya a asusun waje ba tare da wasu sharuda masu tsauri ba ko damar gudanar da al’amura a kasashe masu tasowa.

A ko’ina, masu bayar da tallafi dole ne su cika alkawuransu na kawo ci gaba, kuma dole ne a gyara tsarin bayar da bashi, domin akwai rashin adalci da yaudara a tsarin.

Daga karshe, dole ne taron Sevilla ya tsawatar tare da karfafa kasashe masu tasowa a tsarin kudi na duniya domin biya musu bukatunsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Asuu
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
Labarai

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
majalisar kasa
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
Next Post
Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Jigila Kai Tsaye Zuwa Sin Da Indiya

FCCPC Ta Sammaci Air Peace Kan Rashin Maido Da Kuɗin Tikitin Jirgin Da Aka Soke Tafiyarsa

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.