Shugabancin rikon ƙwarya na jam’iyyar ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tare da sauran mambobin Babban Kwamitin Riƙon Jam’iyar na Kasa, sun gudanar da wani muhimmin taro da shugabannin jihohi 36 da Abuja a Babban Birnin Tarayya, Abuja a ranar Laraba.
An gudanar da taron ne domin kawar da jita-jitar da ke yawo game da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar, tare da ƙarfafa guiwar magoya baya na shirin samar da haɗin kai don tunkarar Jam’iyya mai mulki.
- Har Yanzu A Cikin PDP Nake, Ba Zan Koma APC Ko ADC Ba – Gwamnan Zamfara
- Sauyin Sheƙa Ya Mamaye PDP Da Sauran Jam’iyyu A Borno, Ana Ta Shiga ADC
Da yake zantawa da ’yan jarida bayan taron da aka gudanar, mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa, “Mun gayyato shugabannin jihohi gaba ɗaya domin tabbatar musu cewa ba mu da wani shiri na korar su ko hana su rawar gani. Muna so mu kawar da ƙarya da jita-jitar da ke yawo cewa mun zo ne domin ƙwace jam’iyyar daga hannunsu.”
Abdullahi ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar yana bin tsarin haɗin guiwa, inda ya bayyana shugabannin jihohi a matsayin “abokan aiki wajen gina jam’iyya mai ƙarfi.”
Ya ce taron ya ƙarfafa guiwar shugabannin jam’iyyar a fadin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp