A wani babban ci gaban siyasa gabanin babban taron jam’iyyar PDP na kasa da za a gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo a shekarar 2025, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na Arewa sun amince da tsohon ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, SAN, a matsayin dan takarar da suka amince da shi ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.
An cimma matsayar ne bayan wani gagarumin taron tuntuba da masu ruwa da tsaki n jam’iyyar PDP na Arewacin kasar suka gudanar a Abuja, inda shugabannin jam’iyyar na yankin suka amince da Turaki a matsayin dan takararsu.
A cewar majiyoyi a wurin taron, amincewar na da nufin gabatar da matsayar Arewa guda daya gabanin babban taron da aka shirya gudanarwa daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP.