Hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta gudanar da taro a Litinin din nan, da nufin nazarin halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, tare da tsara dabarun raya ayyukan bunkasa tattalin arzikin kasar a watanni 6 na karshen shekarar bana. Taron ya gudana ne karkashin jagorancin shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Xi Jinping.
Mahalarta taron dai sun yi kira da a aiwatar da ka’idojin raya sassan tattalin arziki bisa dacewa da karsashi, da gaggauta kawar da dokokin da ka iya haifar da koma baya, da kirkiro karin manufofi da ka iya taimakawa cimma burin da aka sanya gaba.
Kaza lika, mahalartan sun yi imanin cewa, ya zama doke a nacewa aiwatar da matakai mafiya dacewa, da manufofin kudi masu inganci, da aiwatar da su bisa gaskiya. Kana a fadada, da kyautata, da inganta, da kuma tabbatar da an aiwatar da manufofin haraji, da na rangwamen biyan kudade, kana a aiwatar da manufofin kudi masu tsari don cimma nasara.
Har ila yau, taron ya amince a karfafa goyon baya, ga fannonin kimiyya da kirkire-kirkiren fasaha, da fannin tattalin arziki na zahiri, da raya kanana da matsakaitan kamfanoni.
Kafin hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a shirya wannan taron, kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin ya shirya wani taron kara wa juna sani domin karbar shawarwari daga wadanda ba ’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ba, da nufin jin ra’ayoyin da suka shafi halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, da ayyukan da ake aiwatarwa na raya tattalin arzikin kasar, a watanni 6 na karshen shekarar nan.
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci zaman taron, tare da gabatar da muhimmin jawabi a ranar Juma’ar da ta gabata.
Cikin jawabin da ya gabatar, Xi ya ce idan ana son gudanar da aikin raya tattalin arziki cikin watanni 6 na karshen shekarar nan yadda ya kamata, ya wajaba a yi aiki da manyan ka’idojin cimma nasarori, tare da wanzar da daidaito.
Ya ce kamata ya yi a kara azama wajen aiwatar da dukkanin sabbin dabarun bunkasuwa ta dukkanin bangarori, da ingiza gina sabon salon ci gaba, da zurfafa cikakkun sauye-sauye da kara bude kofa, da zurfafa amfani da dokoki masu nasaba, da fadada bukatun cikin gida, da bunkasa kwarin gwiwa da kare hadurra.
Daga nan sai shugaba Xi ya jaddada muhimmancin kara azamar ci gaba da kyautata nasarar bunkasar tattalin arziki, da karfafa tasirin karfin dake ingiza nasarar hakan, da fatan al’ummun kasa, kana a ci gaba da dakile asara da boyayyun hadurra, a kuma daga inganci, da fadada nasarorin da ake samu daga tattalin arzikin kasar Sin. (Saminu Alhassan)