Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musu, shugabannin kasashe 26, ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin, da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, da shugaban Iran Masoud Pezeshkian, da shugaban Kongo (Brazzaville) Denis Sassou-Nguesso, da shugaban Zimbabwe Emmerson Dambudzo Mnangagwa, za su halarci bikin tunawa da ranar nasarar yakin turjiyar Sinawa a birnin Beijing, kamar yadda mai taimaka wa ministan harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya sanar a yau Alhamis.
A ranar 3 ga watan Satumba mai zuwa ne dai kasar Sin za ta gudanar da wani gagarumin faretin soji domin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin Japanawa da kuma yaki da mulkin danniya a duniya.
A yau Alhamis ne cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa da aka bude domin shagulgulan bikin, ta gudanar da taron manema labaru na farko na bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin Japanawa da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp