Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya gana da daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) Wang Yi jiya Jumma’a, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Wang Yi ya kai ziyara kasar Habasha ne a kan hanyarsa ta hakartar taron masu ba da shawara kan harkokin tsaron kasa na kasashen BRICS karo na 13, da zai gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
A yayin ganawarsa da Wang, Abiy Ahmed ya yi karin haske kan manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma, yayin da take bin tafarkin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, yana mai cewa, ya yaba da yadda kasar Sin take nacewa kan tafarkin ci gaba da ya dace da yanayin kasarta, gami da saurin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewa da ta samu, wanda ya zama abin koyi ga ragowar kasashe masu tasowa.
A nasa bangaren kuwa, Wang Yi ya bayyana cewa, Habasha babbar kasa ce a nahiyar Afirka da ke da tasiri mai mahimmanci. Yana mai cewa a matsayinsu na abokan huldar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, Sin da Habasha suna da buri daya, kuma sun gudanar da hadin gwiwa mai inganci bisa tsare-tsare irin su “shawarar ziri daya da hanya daya” da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ke jagorantar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Ban da haka, Wang Yi shi ma ya gana da mataimakin firaministan kasar Habasha kuma ministan harkokin wajen kasar Demeke Mekonnen.
Yayin ganawar, Wang ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Habasha wajen kiyaye ikonta mulkin da cikakkun yankunanta, da goyon bayan kasar wajen cika alkawarin da ta dauka na tabbatar da hadin kai da zaman lafiyar kasar, tana kuma goyon bayanta wajen taka muhimmiyar rawa a harkokin shiyya-shiyya da na kasa da kasa.
Ya kara da cewa, Sin na son yin aiki tare da Habasha wajen aiwatar da manufar zaman lafiya da ci gaba a yankin kahon Afirka, da tallafa wa jama’ar Afirka wajen warware matsalolin Afirka ta hanyar da ta dace da Afirka.
A nasa bangaren, Mekonnen ya bayyana cewa, kasar Habasha tana da dadadden tarihi wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana da niyyar karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a matakan kasashen biyu, da shiyya-shiyya da kuma sassa daban-daban.
Ya ce, Habasha ta yaba da irin taimakon da kasar Sin take ba ta, wajen kiyaye tsaro da zaman lafiyarta, tana kuma fatan kasar Sin za ta kara taimaka mata wajen tabbatar da zaman lafiya, da aiwatar da gyare-gyare, da ma farfado da tattalin arzikinta yadda ya kamata.
Bugu da kari, shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto, ya gana da Mr. Wang Yi a birnin Nairobi na kasar Kenya a yau Asabar, inda bangaorin 2 suka bayyana niyyar raya huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon mataki. (Ibrahim Yaya, Bello Wang)