A daren jiya Alhamis 16 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gudanar da wani karamin rukunin tattaunawa tare da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a nan birnin Beijing, inda suka yi musayar ra’ayoyi sosai kan batun Ukraine.
A yayin tattaunawar, Xi Jinping ya bayyana matsayin da kullum kasarsa ke tsaye a kan sa, da ma kokarin da take yi wajen ganin an warware rikicin Ukraine ta hanyar siysa. A cewarsa, muhimmiyar mafita ga rikicin Ukraine shi ne inganta gina wani sabon tsarin tsaro mai daidaito, da inganci, da dorewa. Ya ce kasar Sin tana goyon bayan gudanar da taron zaman lafiya na kasa da kasa a kan lokaci, wanda kasashen Rasha da Ukraine suka amince da shi, tare da halartar dukkanin bangarori, da tattaunawa cikin adalci kan dukkan shirye-shiryen da aka gabatar, kuma kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa game da warware matsalar Ukraine ta hanyar siyasa ba tare da jinkiri ba.
A nasa bangaren, shugaba Putin ya gabatar da matsayar Rasha kan wannan batu, inda ya ce kasarsa ta yaba da matsayin kasar Sin mai adalci, da daidaito kan batun Ukraine. Ya kara da cewa, Rasha na kokarin warware matsalar Ukraine ta hanyar siyasa, kuma tana son nuna sahihanci, tare da ci gaba da yin mu’ammala da kasar Sin kan wannan batun. (Mai fassara: Bilkisu Xin)