• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Kasashen Tsakiyar Asiya Sun Yi Alkawarin Kara Hadin Gwiwa Da Sin

by CMG Hausa
2 years ago
Asiya

Shugabanni daga kasashen tsakiyar Asiya, sun jaddada muhimmancin shawarar ziri daya da hanya daya, BRI a takaice, tare da bayyana goyon bayansu ga sanarwar Xi’an, yayin taron kolin kasashen Sin da tsakiyar Asiya da aka yi jiya Jumma’a a birnin Xi’an na lardin Shaanxi dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin.

Shugabannin sun kuma yi tsokaci sosai kan ra’ayin shugaban kasar Sin Xi Jinping, na gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama, da shirin raya kasa da kasa, da samar da tsaro a duniya, da shirin wayewar kai a duniya.

  • Babban Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Na Kasar Sin Ya Gana Da Manyan Mambobin Kungiyar Musulmai Ta Kasar Sin

Za kuma su yi amfani da bikin cika shekaru 10 da kirkiro shawarar, a matsayin wata dama ta inganta hadin gwiwa a shiyyar, da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban, da kara kusanto da al’ummar Sin da tsakiyar Asiya mai makomar bai daya.

Game da wannan taron kolin shugabannin kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya da aka shirya a birnin Xi’an, fadar mulkin lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin tsakanin ranakun 18 zuwa 19, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya zanta da manema labarai jiya, inda ya bayyana cewa, matsayar da aka cimma game da gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen tsakiyar Asiya babban sakamakon siyasa ne da aka samu yayin taron.

Qin Gang ya yi tsokaci da cewa, taron kolin yana da ma’anar tarihi saboda, shi ne karo na farko da aka kira taron, tun bayan da aka kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya shekaru uku da suka gabata.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

Kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi yayin taron, inda ya gabatar da matakai hudu kan yadda za a gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen tsakiyar Asiya ta bai daya, kana ya gabatar da shawarwari guda takwas kan hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, wannan shi ne karo na farko da shugaban kolin kasar Sin ya yi cikakken bayani kan manufofin huldarta da kasashen yankin tsakiyar Asiya a sabon zamanin da ake ciki, manufofin da suka samu yabo da amincewa matuka daga shugabannin kasashen yankin da suka halarci taron.

Hakazalika kasar Sin da kasashe biyar dake yankin tsakiyar Asiya, sun sa hannu kan takardu guda bakwai wadanda suka hada da “sanarwar Xi’an ta taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya”, da “sakamakon taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya” da sauransu, kana sun daddale yarjejeniyoyi sama da 100 dake shafar fannoni daban daban, ana iya cewa, tasirin taron kolin, yana da girma kuma ba a taba ganin irinsa a tarihi ba.

Ban da haka, Qin Gang ya jaddada cewa, kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya, ba za su mayar da wata kasa saniyar ware ba yayin da suke gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, kuma za su yi kokari tare da sauran kasashen duniya, domin ingiza ci gaban duniya baki daya.

Sannan a yau Asabar, kafar CMG ta sharhanta cewa, an yi nasarar shirya taron kolin shugabannin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya guda biyar karo na farko, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi yayin taron, inda ya jaddada cewa, duniyarmu tana bukatar yankin tsakiyar Asiya mai kwanciyar hankali da wadata da zaman jituwa dake cudanyar juna, kana ya gabatar da matakai hudu kan yadda za a gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen tsakiyar Asiya ta bai daya, kana ya bayar da shawarwari guda takwas kan hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, duk wadannan sun samu yabo da amincewa matuka daga shugabannin kasashen yankin mahalartan taron.

Taron ya kasance taron da kasar Sin ta kira a zahiri na farko, tun bayan da ta kulla huldar diplomasiyya da kasashen yankin tsakiyar Asiya, kana shi ne taron koli karo na farko da ta kira tun bayan da aka kafa tsarin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya shekaru uku da suka gabata.

A halin yanzu duniyarmu tana fama da manyan sauye-sauye, don haka kasar Sin da kasashe biyar dake yankin tsakiyar Asiya, suna fuskantar jarrabawa mai sarkakiya, kuma dukkansu suna kokarin raya kasashensu, shi ya sa huldar dake tsakaninsu tana kara zurfafa yadda ya kamata.

Kamar yadda shugaba Xi ya fada wato gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen tsakiyar Asiya ta bai daya, zabi ne mai ma’anar tarihi da suka yi bisa la’akari da babbar moriyar al’ummomin kasashen da makomarsu mai haske. (Mai fassarawa: Ibrahim Yaya, Jamila Zhou)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Daga Birnin Sin

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Next Post
Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Dawo Nijeriya Gabanin Rantsar Da Shi

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Dawo Nijeriya Gabanin Rantsar Da Shi

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.