A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaran aikinsa na kasar Argentina Alberto Fernández sun mika wasikar murnar bude taron dandalin tattaunawa kan musayar al’adu tsakanin kasashen biyu.
A cikin wasikar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Argentina.
A cikin rabin karnin da ya gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta himmatu wajen tinkarar kalubalen da kasashen duniya suke fuskanta, kana ta zama abin koyi na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a fannonin hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare.
Xi Jinping ya yi fatan mahalarta taron, za su yi musayar ra’ayoyi da cimma daidaito don sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Argentina, kana za su ba da gudummawa wajen gina al’ummar Sin da Latin Amurka mai kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani.
A nasa bangare, shugaba Fernández ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, kasashen biyu sun yi hadin gwiwa har na tsawon rabin karni, kuma ya yi imanin cewa, kasashen biyu za su samu kyakkyawar makomar bai daya a nan gaba. Kana hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen biyu, ta sa kaimi ga fahimtar juna tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Zainab)