A daren ranar 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaran aikinsa na kasar Italiya Sergio Mattarella sun kalli kayayyakin tarihi da aka dawo da su kasar Sin.
Shugaba Mattarella ya yi bayani ga shugaba Xi game da kayan tarihi na al’adun Majiayao dake wakiltar kayayyakin tarihin da Italiya ta mayar da su ga kasar Sin.
- Babbar Majalisar Dokokin Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Abin Da Ake Kira Dokar Yankunan Teku Na Philippines
- Yadda Donal Trump Ya Lashe Zaben Shugabancin Amurka
Xi Jinping ya bayyana cewa, lokacin da ya ziyarci Italiya a shekarar 2019, Italiya ta dawo da kayayyakin tarihin Sin 796 da aka kwashe ba bisa doka ba, hakan ya bude sabon babi na hadin gwiwar kasashen biyu a fannin kayan tarihi na al’adu, da kasancewa sabon abin misali na dawo da kayayyakin tarihi ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. A wannan karo, Italiya ta kara dawo da kayayyakin tarihin Sin guda 56, wannan ya nuna girmamawa ga al’adun kasar Sin, da kuma sada zumunta a tsakanin Sin da Italiya.
A wannan rana da dare, Xi Jinping ya ba Mattarella wani kayan ado a teburi mai siffar na’urar bincikin duniyar wata ta Chang’e-5, da kuma samfuran abubuwan da aka samo daga duniyar wata a matsayin kyauta. Kana Xi da matarsa Peng Liyuan sun kalli bikin kide-kiden Giacomo Puccini tare da shugaba Mattarella da diyyarsa. (Zainab Zhang)