Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kongo Brazaville Denis Sassou Nguesso, sun aike da wasiku na taya murna ga taron ministocin kula da harkokin da suka shafi aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC, inda suka taya murnar bude taron.
Cikin sakonsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, yanayin kasa da kasa ya cika da sauye-sauye da hargitsi. Kuma kasar Sin ta dage wajen samar da sabbin damammaki ga duniya tare da sabbin nasarorin da aka samu na zamanantarwa iri ta kasar Sin, da samar da sabon kuzari ga kawayen kasashe masu tasowa na duniya kamar kasashen Afirka ta hanyar shiga a dama da su a babbar kasuwarta. Kasar Sin tana son yin shawarwari da rattaba hannu kan yarjejeniyar huldar abokantaka ta raya tattalin arziki tare, da aiwatar da manufar soke haraji da kaso 100 bisa 100 kan wasu hajojin dake shiga kasar daga kasashen Afirka guda 53 masu huldar diplomasiyya da ita, sa’an nan kuma za ta samar da karin sauki ga kasashe masu karamin karfi na Afirka don fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin.
- Manchester City Ta Kammala Daukar Rayan Cherki Daga Lyon
- Nan Ba Da Jimawa Ba Harkar Man Fetur Za Ta Sauya A Nijeriya – Dangote
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yana fatan kasashen Sin da Afirka za su ci gaba da sa kaimi ga aiwatar da sakamakon taron kolin, da tsara yadda za a bunkasa dandalin a nan gaba, da yin hadin gwiwa don gina al’umma mai makoma ta bai-daya ta Sin da Afirka a sabon zamani, da ba da gudummawar karfin Sin da Afirka wajen gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai-daya ga daukacin bil’adama.
A cikin wasikar taya murnar, Sassou ya bayyana cewa, tun bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a nan birnin Beijing, an samu sakamako mai kyau na hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin. Kana ya ce, zai ba da himma tare da shugaba Xi Jinping ba tare da kakkautawa ba, don sa kaimi ga samun babban ci gaba a fannin gina al’umma mai makomar bai-daya ga Afirka da Sin, da kuma kara kyautata jin dadin jama’ar bangarorin biyu. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp