A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Madagascar Andry Rajoelina, suka taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen su.
Cikin sakon sa, shugaba Xi ya ce tun kafuwar wannan dangantaka shekaru 50 da suka gabata, alakar sassan biyu ta ci gaba da kyautatuwa bisa daidaito, duk da sauye sauyen da ake samu a harkokin kasa da kasa.
Ya ce yana dora muhimmancin gaske ga alakar dake tsakanin ta da Madagascar, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Rajoelina, wajen amfani da wannan biki, a matsayin wata dama ga kasashen, ta ci gaba da daga matsayin hadin gwiwar kawancen su, da baiwa kasashen da al’ummun su damar cin gajiya.
A nasa bangare kuwa, shugaba Rajoelina cewa ya yi, tun kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar sa da Sin shekaru 50 da suka gabata, sassan biyu sun fadada hadin gwiwar su a sassa daban daban, an kuma cimma manyan nasarori masu yawa.
Ya ce Madagascar a shirye take, ta yi aiki da Sin wajen karfafa manufar samar da al’umma mai makomar bai daya ta Madagascar da Sin. (Saminu Alhassan)