Da yammacin yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta kafar bidiyo.
Yayin zantawar su, Xi Jinping ya nuna cewa, a watanni 11 da suka gabata, yawan kudin dake shafar cinikayyar Sin da Rasha ya kai sabon matsayi, kuma sassan 2 sun yi hadin kai a wasu manyan fannoni yadda ya kamata. Ya ce kwanan baya, Sin ta daidaita manufarta ta kandagarkin cutar COVID-19 bisa halin da ake ciki, tare da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar, matakin da ya sa aka karkata babban aiki zuwa kiyaye lafiyar jama’a, da kare mutane daga kamuwa da munanan cututtuka.
Shuga Xi ya kara da cewa, Sin na fatan yin hadin kai da kasashen duniya, ciki har da Rasha a fannin maido da tuntuba tsakanin al’ummun su bisa tsari. Xi ya kuma nanata cewa, Sin na fatan hadin kai da Rasha, da ma sauran kasashen duniya, don yaki da manufar babakere, da manufar kare kai da ta kariyar cinikayya, da kuma nacewa ga kare ikon mulkin kai na kasashen biyu, da tsaro, da muradu, da kuma adalci da daidaito a duniya.
A nasa bangare, shugaba Vladimir Putin ya ce, a halin yanzu ana fuskantar yanayi mai sarkakkiya a duniya, amma duk da haka, huldar kasashen biyu na bunkasuwa yadda ya kamata, kuma suna ingiza hadin kai a fannin makamashi, da ayyukan gona, da zirga-zirga, da manyan ababen more rayuwa, da motsa jiki, da al’adu da sauransu.
Ya ce Rasha na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan ra’ayin kasar Sin game da batun yankin Taiwan, da nacewa ga ka’idar kasar Sin daya tak a duniya. Har ila yau, Rasha ta amince cewa, za a iya inganta tuntubar al’umomin kasashen biyu bisa sabuwar manufar kandagarkin annobar da Sin ta dauka.
Ban da wannan kuma, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra’ayi kan rikicin Ukraine. Game da hakan, Xi Jinping ya nanata cewa, Sin ta lura cewa, Rasha ba ta taba kin yarda da warware rikicin Ukraine ta hanyar shawarwari ba, kuma Sin ta yaba da hakan. Kaza lika Sin za ta ci gaba da nacewa gaskiya da adalci, da ingiza hadin kan al’ummar duniya, don taka rawa wajen warware rikicin cikin lumana. (Amina Xu)