Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwararsa ta kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kafa dangantakar diplomasiyyar kasashen su.
A sakon nasa, shugaba Xi Jinping ya ce a shekarun baya bayan nan, kasashen biyu na ci gaba da inganta amincewa da juna a siyasance, da samun ci gaba mai armashi a fannin hadin gwiwar bangarori daban-daban, matakin da ya zama abin koyi a hadin kan kasashe masu tasowa.
- Sakamakon Binciken CGTN Ya Karkata Ga Goyon Bayan Tsagaita Wuta Da Kawo Karshen Yaki Tsakanin Falasdinu Da Isra’ila
- Xi Jinping Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken
Shugaban na Sin ya kara da cewa, a mafarin sabon tarihin da za a kafa, yana fatan kara hadin kai da shugaba Samia Suluhu Hassan, don zurfafawa, da habaka ma’anar huldar abokantaka tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za su taka rawar gani wajen daga matsayin kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya ta Sin da Afrika.
A nata bangaren kuma, shugaba Samia Suluhu Hassan ta ce, Tanzaniya na jinjinawa ci gaban da ba a taba gani ba a karnin da muke ciki wanda Sin ta samu a bangarorin raya tattalin arziki da al’umma, kuma tana godiya ga taimakon da Sin take baiwa bunkasuwar kasar. Ta ce, kasar za ta yi tsayin daka wajen tabbatar da aiwatar da wasu manyan shawarwari, ciki har da “ziri daya da hanya daya”, da shawarar samun bunkasuwar duniya baki daya, da ma karfafa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakanin kasashen Sin da Tanzaniya daga dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare-tsare. (Amina Xu)