Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai.
A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu ga muhimmin matsayin shugaba Xi a kwamitin kolin JKS da ma jam’iyyar baki daya.
Kazalika, sun bayyana fatan ‘yan jam’iyyar da sojoji da jama’ar dukkan kabilu za su kara hada kai da kara kusantar kwamitin koli na jam’iyyar tare da kwamared Xi Jinping a matsayin jigon gina kasar Sin zuwa kasa mai matukar karfi da kuma cimma nasarar farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanatarwa irin ta Sin. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp