Wazirin Katsina na 5, Ferfasa Sani Abubakar Lugga ya yi kira da kakkausar murya ga manyan jami’an tsaron Nijeriya da su ajiye mukamansu tunda sun kasa kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Ferfasa Lugga ya bayyana haka ne a lokacin wata lakca da kungiyar yan jaridu ta ƙasa, NUJ reshen jihar Katsina suka shirya a ɗaya daga cikin bukukuwan cikar jihar Katsina shekaru 37 da kafuwa.
- Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bikin Cikar Daularsu Shekaru 94 Tare Da Karfafa Alaka Da Nijeriya
- Rahoto: Masana’antun Ɗab’i Na Dijital Na Kasar Sin Sun Haɓaka Cikin Sauri A 2023
Lugga ya ƙara da cewa, dole a samo jami’an tsaro masu kishin ƙasa waɗanda za su maye gurbin waɗanda suka kasa kawo ƙarshen wannan matsala.
“Hakkin jami’an tsaro ne musamman sojoji da ‘Yansanda su kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu, kuma dole su gano hanyar da Nijeriya zata zauna lafiya” inji shi
Ferfasan ya ce, ba daidai bane a cewa al’umma, su nemi makami su ƙare kansu daga harin ‘yan bindiga, haka bata taɓa faruwa ba a tarihi, sannan idan aka bari wannan abin ya ci gaba za a haifar da gagarumar matsala.
A cewarsa, tunda gwamnatin tarayya ta ƙasa kawo ƙarshen wannan matsala, to dole kundin tsarin mulkin Nijeriya a gyara shi domin ya bai wa jihohi damar yin ‘yansanda na su na kansu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp