A makon da ya gaba ne, Shugabar Matan Jam’iyyar NNPP reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, Hajiya Saudat Abdullahi, ta karbi bakuncin shugaban jam’iyyar na kasa a sakariyar jam’iyyar ta Abuja, yayin da ya kai ziyara sakatariyar domin jinjina musu kan namijin kokarin da suke yi na ganin jam’iyyar ta sake samun karbuwa.
A jawabin da ya gabatar, shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Ahmed Rufa’i Alkali, ya ce sun zo domin ziyara ta musamman ga ‘yan jam’iyyar da kuma kara musu kwarin gwiwar ci gaba da kokarin da suke yi na ganin an kai ga cimma nasarar abin da suka sa a gaba.
“Mun zo ne mu ga wannan ofis ne na mutanenmu dake FCT wanda kuma ka san cibiyar kasa ce.
Mutane ne masu kishin wannan jam’iyya kuma sun yi abubuwa da dama na kasaita, shi ne muka ya dace mu zo, don haka shugabannin wannan jam’iyya na kasa gaba daya muka hallara a nan domin mu jinjina musu, kuma mu gaisa da su.
Sannan muna rokonsu da su ci gaba da aiki mai kyau, musammam magana neman mambobi, kada a karaya, a ci gaba da neman jama’a in kuma an same su to a ci gaba jan hankalinsu da su yi rajista, rajistar jam’iyya da kuma rajistar INEC wato wacce za su yi zabe da ita,” in ji shi.
A cewarsa, dalilin da ya sa ya sa a yi rajistar zabe, idana aka zo zabe katin zaben nan shi aka sani, in baka da shi to ba za ka amfani kowa ba, to gaskiya mun gode da irin yadda shi Alhaji Dauda shugaban jam’iyya na FCT da kuma Hajiya Saudat shugabar mata suke nunawa da sauran jama’arsu, Allah ya saka musu da alheri.
A zantawarta da wakilimmu bayan kammala ziyarar, Shugabar Matan Jam’iyyar ta NNPP ta Babban Birnin Tarayya Abuja, Hajiya Saudat Abdullahi, kira ta yi ga jama’a musamman mata dake fadin tarayyar kasar nan da su tabbataba sun karbi katin zabe, domin a cewarta akwai jam’iyyu kamar APC da PDP, wadanda tuni sun taka rawarsu ta fuskar gudanar da shugabancin kasar nan kowa ya gani ya kuma shaida abin da suka yi, kuma mun ga yadda suka mayar da kasar, an mayar da mutane kamar ba mutane ba, kasa babu tsaro, tattalin arzikin ya karye, ga tsadar abubuwan yau da kullum, ga bashi ya yi wa kasar katutu.
A don haka ta ga dacewar kira gare su da kada su yi kasa a gwiwa wajen ganin sun riki katin zabensu domin sai da katin zabe ne mutum zai iya sauya gwamnatin da yake son canjawa.
Da aka tambaye ta ko yaya take ganin karbuwar jam’iyyar a babban birnin tarayya, duba da cewa akwai manyan jam’iyyu a gabansu? Sai ta ce, eh lallai haka ne, akwai jam’iyyu manya kamar PDP da APC wacce a yanzu ke mulki, to ai kasancewarsu manyan jam’iyyu ba shi yake nuna kullum su za su ci gaba mulki a kasar nan ba, domin kuwa an yi wata jam’iyya da yi mulki a baya kamar NPN karkashin shugabancin Marigayi Shehu Shagari, to yanzu ina NPN take, ka ga ta wuce, don haka duk abin da ya yi zamaninsa yana iya kaucewa ya bar wa wani shi ma ya yi nasa zamanin, saboda haka yanzu NNPP ta yunkuro kuma babu gudu babu ja baya, za ta ba wa mamaki domin shi mulki na Allah kuma a wurin Allah muke nema, in sha Allah za mu yi nasara.
“Wannan jam’iyya ta shigo ne da nufin in har Allah ya sa muka kafa gwamnati za mu mayar da Nijeriya ta zama sabuwa, ta hanyar samar da ingantaccen tsaro, mutum zai yi tafiya kamar yadda ake yi a baya ba tare da jin wata fargaba ba, sannan kuma ilimi da shi ma a yanzu yake cikin halin ha’ula’i dole a yi gyara, da kuma samar da hanyoyin da za’a tallafa wa mata matasa da yara domin su tsaya da kafarsu, kuma hakan za a yi ne ba tare da nuna banbancin kabila addini ko bangaranci ba“, in ji ta.
Ta yi kira ga mata da su rungumi jamíyyar NNPP domin ita ce jam’iyyar da take burin fitar da talakawa daga mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki na talauci da fatara.
“Ina kira ga mata da su fito kwansu da kwarkwatarsu, domin wannan jam’iyyar tasu ce, kuma har yanzu a rajista ba a rufe ba, su adana saboda ranar zabe su fito domin kada kuri’arsu.
Mun karbi mata da yawa da suke da wannan rajista, wadanda ba su da ita muna umartar su da su je yanki ta su rajistar, domin an sake kara lokaci, don haka ina kira ga mata da su yi tsayin daka wajen ganin sun yi wannan babban zabe tanadi, ya zama muna tare da su ko ina madugu zai tafi muna tare kafarsa kafarmu”, in ji ta.
Ta ci gaba da cewa a wannan tafiya ta mudugu idan har Allah ya sa mun kai ga samun nasara, to kowa za a yi masa abin ya dace domin Nijeriya aka ce, duk dan Nijriya kuma ya cancanci a kyautata masa, sawa’un daga Kudu yake ko Arewa babu banbanci in dai dan Nijeriya ne, kuma duk ayyukan da aka yi a kowace jiha shi za a yi a sauran jihohin. Sannan ta yi kira ga dukkan mambobin jam’iyyar da su ci gaba da jajircewa wajen nuna kishi da son jam’iyyar, sannan su guji nuna banbanci na kabilanci ko bangaranci, kazalika ta yi kira ga matasa da guji shiga siyasar daba, da ta’ammali da miyagun kwayoyi, a cewarta yin ta’ammali da miyagun kwayoyi shi kan sanya su afkawa cikin haramtattun kungiyoyi.
A karshe ta yi addu’ar Allah ya zaunar Nijeriya lafiya, ya kawo yalwal arziki, ya ba wa jama’iyyar NNPP nasara a dukkan al’amuran da ta sa a gaba.