Shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ta kaddamar da cibiyar cinikayya da jigila ta gabashin Afrika, wani ginin da ya sauya tsarin jigila da cinikayya da kamfanin kasar Sin na EACLC LIMITED ya yi a kasar.
Da take jawabi yayin kaddamar da cibiyar a ranar Jumma’a a birnin Dar es Salaam, shugaba Samia Hassan ta bayyana cibiyar da ta lakume dala miliyan 170 a matsayin wani muhimmin jari dake da nufin inganta cinikayya da hade yankin gabashin Afrika da kuma zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Tanzania.
- ADC Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM A Neja
- Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Ta kara da cewa, cibiyar za ta karfafa dangantakar Tanzania da kasuwannin dake cikin kasuwar bai daya ta yankin gabashi da kudancin Afrika.
A nata bangare, shugabar kamfanin EACLC na kasar Sin Wang Xiangyun, ta ce cibiyar mai fadin sama da murabba’in mita 75,000 mai dauke da shaguna 2,060, ita ce irinta mafi girma a Tanzania.
Ta kara da cewa, cibiyar ta hada ayyuka daban-daban karkashin dandali guda kamar wuraren adana kayayyaki ba tare da biyan haraji ba da na aikin kwastam da cinikayya ta intanet da tsarin biyan kudi kafin sayen kayayyaki da sake fitar da kayayyaki, tana mai cewa, ana sa ran cibiyar za ta rage kudin da ake kashewa na cinikayya a yankin da kaso 30, da samar da gurabun ayyuka 50,000 da karin kudin shiga da zai taimaka wa ci gaban kasar. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp