A Siffar Annabi (SAW) da kyawonsa, kowacce gaba ta dace da inda aka ajiye ta. Yana daga cikin Hadisin da aka karbo daga Sayyidina Ali da Anas bin Malik Kadimin Manzon Allah (SAW) da Abi Hurairata da Barra’u da Sayyada A’isha Uwar Muminai da dan Abi Halata – dan Sayyada Khadijah uwar Muminai da Abi Juhaifat da Jabir dan Samurata da Ummu Ma’abadin da Abdullahi bin Abbas da Abis Suhaili da Kuraimu bin Kafitin da Hakimu bin Hizamu da sauransu.
Manzon Allah SAW ya kasance mai hasken launi ne, mai farin ido, mai bakar kwayar ido ko kuma a ce mai gaza-gazan ido, mai yalwan ido, sannan akwai ja-ja a cikin farin idon, mai yawan gashin ido, mai hasken goshi, mai zananniyar/hadaddiyar gira, mai kewayayyiyar fuska, mai yelwar goshi, mai kaurin gemo, mai daidaiton ciki da kirji, mai yalwan kirji, mai girman kafadu, mai girman kashi, mai girman damtse, mai yalwan tafi da digadigi, mai tsawon yatsu, mai tsawo ne, mai sakakken gashi, idan ya bude baki zai yi dariya sai ka ga haske kamar walkiya kuma kai ka ce hakoransa kamar kankara, mai madaidaicin wuya, mai daurarren jiki.
Sahabi Barra’u yana cewa “Ban taba ganin mutum mai gashin kai da yawa har ya zuba a gadon baya a cikin jajayen kaya wanda ya fi Annabi (SAW) kyau ba”
Abi Huraira yana cewa “Ban taba ganin wani abu mai kyau ba kamar fuskar Annabi Muhammad (SAW), kai kace Rana ce take jujjuyawa a fuskarsa, idan ya yi murmushi sai ka ga hasken hakoransa kamar yana bugan bango.”
Kuma duk abin da wadannan sahabbai suke fada, suna fadar abin da suka gani ne ba wai suna fada kawai don soyayya ba ne.
Sahabin Shehu Ibrahim Inyass, Barham Job yake fada, irin fuskokin Annabawa da ake fada, musamman fuskar Annabi Muhammad (SAW), da fuskar bayin Allah da ake fada, to in ba ka riski fuskokinsu ba ka ga ta Shehu Ibrahim Inyass, za ka gan shi Karamatan. Saboda fuskar Shehu, fuska ce mai ganin Annabi Muhammad (SAW) sannan kuma ga hasken Ma’arifa.
Jabiru dan Samurata ya ce, wani mutum ya tambaye shi cewa, “An ce fuskar Annabi kamar hasken takobi take?” Sai ya Jabiru ya ce “A’a, kamar hasken Rana take da Wata, sannan kuma fuskarsa kewayayya ce.”
Ummu Ma’abadin wata mata ce mai kyauta, ta kasance tana kafa rumfa ta zauna a ciki tana taimakon mutane. Wata rana sai Annabi Muhammad (SAW) da Sayyidina Abubakar da Abdullahi bin Umar suka biyo ta wajen rumfarta, bayan sun zauna sun huta sai suka nemi ta ba su nonon tumaki in tana da shi, sai ta ce musu duk sun fita kiwo, sai dai daya ta rage kuma ba ta da lafiya, hakan ne ya hanata fita kiwo, sannan kuma yarinya ce ba ta da hantsa. Sai Annabi (SAW) ya ce mata, in tayar da su na tatsa ba matsala, sai ta ce ta yarda, Annabi ya nemi a kawo wajen tara nonon. Bayan ya yi addu’a, sai ya fara ba ta ta sha bayan ya tatsa, sannan suka sha, ya kara tatsa ya zuba mata a kwaryarta sannan ya yi Addu’a hantsa ta koma inda take. Bayan mijinta ya dawo ya ga nono, ya tambaye ta a’ina ta samo, sai ta ba shi labarin duk abin da ya faru, ta ce “kuma ina zaton mutumin nan ne da Kuraishawa suke nema,” sai mijin ya ce siffanta min shi. A nan ne aka samo hadisin sioffofin Manzon Alllah (SAW) daga Ummu Ma’abadin.
Ta fada daga cikin siffofin da ta siffanta Annabi da shi, tana cewa “shi ne mafi kyawun mutane in yana nesa, mafi dadin kallo kuma in yana kusa da kai.”
A cikin hadisin dan Abi halata, ya fada yana cewa “fuskar Annabi za ka gan ta tana kyalkyali, irin kyalkyalin wata dan daren Shahudu.”
Sayyidina Aliyu, Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, wanda ya ga Annabi ba tare da ya yi zaton ganin sa ba, ba ka san da zuwansa ba kawai jim kuka hadu, sai ka razana sabida kwarjininsa, wanda kuma yake zaune tare da shi zai ji soyayyar Annabi tana ta kara shigansa.
Mai siffanta Annabi yana cewa ban taba gani ba kafin Annabi ko bayansa wani irin sa.
Hadisai masu siffanta Annabi ba za su kidayu ba sai dai za mu tsaya haka da wadannan da muka ambato.
Yanzu bari mu juya zancenmu daga siffofinsa zuwa Tsaftarsa Annabi Muhammad (SAW). Tsaftar Annabi da kamshin jikinsa, da kamshin iskar jikinsa, da kamshin zufar jikinsa, da nesantarsa da kazanta, da nesantarsa da duk wani aibu na jiki. Hakika Allah ya kebance shi da wasu kebance-kebance wadanda ba a samu ba a wurin waninsa sannan Allah ya cika ta da tsaftar Shari’a da dabi’a ta halitta.
Duk Annabawa, Allah ya halicce su a kan dabi’u guda goma: Kaciya, Askin gashin mara, Tsige gashin hammata, Yanke farce, Datse gashin baki, Cika gemu, Gyaran gashin kai in an barshi, da rashin aske furfura – akwai karin bayani a wurin malamai, amafani da turaren ruwa sai kuma yin amfani da turaren wuta. Wadannan guda goma su ake kira da Fidra.
Manzon Allah (SAW) ya ce “an gina Addini a kan Tsafta.”
Sufyan bin Asi da waninsa sun zantar da mu daga Umar bin Umar har zuwa kan Anas bin Malik, shi kuma yace ban taba shakan turaren anbar ko Miski ko wani abu mai dadin kamshi ba wanda yafi kamshin iskar Annabi Muhammad (SAW) ba.
An karba daga Jabir dan Samurata cewa wata rana Annabi Muhammad (SAW) ya shafi kuncin Jabiru, sai Jabiru ya ce, na samu (na ji) tafin hannun Annabi mai sanyi da kamshi kai ka ce ya fito da hannunsa ne daga kwalbar mai sayar da turare. Waninsa ya ce hannun Annabi kamshi ce da ita, ya shafa mata turare ko bai shafa ba.
Da yawa Annabi yana musabaha da mutane amma duk wanda aka yi musabaha da shi hannunsa za ta yi ta yin kamshi ko da ya wanke hannunsa sau da da yawa, da yawa kuma Annabi yake shafan kawunan yara, sai kan ya yi ta kamshi, har akan iya gane Annabi ya shafi kan yaro in an ji kan yaron yana kamshi a tsakanin ‘yan uwansa.
Wata rana Annabi (SAW) ya yi bacci a gidan Ummu Sulaim mahaifiyar Anas, sai Annabi ya yi zufa, sai Ummu Sulaim ta zo da kwalba tana tara gumin Annabi a cikinta, sai Manzon Allah ya farka ya gan ta a haka, bayan ya tambaye ta da cewa Ummu Sulaim me kike yi ne haka, sai ta ce ya Rasulullah muna hada shi ne da turaren mu, in muka yi haka, turarenmu yana zama wanda ya fi na kowa kamshi.
Akwai wani sahabi na Annabi da yake da cutar warin kashi, ya kai kuka wurin Annabi kan cutar da ta dame shi, sai Annabi ya ce masa ya yi kunzugu, Annabi ya shafi duk jikinshi, take jikinshi ya fara kamshi. Sabida hannun kamshi ne na Annabi.
Imam Bukhari ya fada a cikin littafin tarihinsa daga Jabiru cewa idan Annabi ya bi hanya wani mutum ya bi hanyar sai ya san Annabi ya bi hanyar sabida kamshin da yake zama a kan hanyar, sabida Annabi ya bi hanyar.
Ishak bin Rahawaihi ya fada cewa duk wannan kamshin da ake fada na jikin Annabi ne ba wai na turare ba ne. Haka kuma Mallam Muzammili da Harbi duk sun ruwaito Hadisi daga Jabiru, Jabiru yake cewa, Annabi ya goya ni a bayan Jakinsa, sai na dinga sa hatimin annabtarsa a bakina, sai hatimin ya dinga tashin kamshi a cikin bakina.
Masu kula da tarihin Annabi (SAW) sun yi hikaya cewa idan Annabi yana son ya yi bayin gida, kasa ce da take budewa ta hadiye bayan gidansa da fitsarinsa, sannan a ji iska mai kamshi ta tashi.
Muhammad bin Sa’ad, Marubucin imamul wakidi ya yi isnadin Hadisi daga kansa har izuwa Sayyada A’isha, Sayyada A’isha tace “ya Rasulullah kana zuwa yin bayan gida amma in mun je mun duba ba ma ganin komai, sai Annabi Ya ce Ya A’isha ba ki sani cewa kasa tana hadiye duk abin da ya fito daga cikin Annabawa ba, ba za a ga komai ba”. Wannann Hadisi ko bai zama Mashhuri ba, hakika Malamai ma’abota Ilimi sun fada cewa bayan gidan Annabi da bawalinsa tsarki ne tun da komai na Manzon Allah abin so ne, to haka ma bayan gidansa da bawalinsa duk daga wajensa suke.
Yana daga cikin Hadisin Sayyidina Aliyu na wafatin Annabi da yake cewa na wanke Annabi sai na tafi in duba abin da yake futa daga Mamaci sai na samu cewa babu komai, sai nace “Ya rasulullah ka tsarkaka mamaci kamar yadda ka tsarkaka a raye, sai wani kamshi ya taso min ban taba jin kamshi irin wannan ba.”
Sayyidina Abubakar ya fada irin wannan Hadisi ya yin da ya sumbanci goshin Annabi bayan rasuwarsa, ya ce “Ya Rasulullah ka tsarkaka kana raye da kana a mace”.
Yana daga cikin abin da zai nuna maka kamshin Annabi da duk abin da ya futa a jikinsa, shan jininsa da Imam Malik bin Sinanin, Abi Kudri a ranar yakin Uhudu.