Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang, ya ce kasar sa a shirye take ta karfafa musaya, da tallafawa ci gaban kasar Gambia.
Qin Gang, wanda ya bayyana hakan a yau Juma’a ga takwaransa na Gambia Mamadou Tangara, a gefen taron “Lanting” na bunkasa zamanantar da Sin da duniya, ya ce Sin na kara azamar aiwatar da cikakken salon zamanantar da kai, wanda zai haifar da manyan damammakin ciyar da al’ummun duniya, ciki har da na Gambia gaba.
Da yake mayar da jawabi, Mr. Tangara, ya tabo batun ziyarar baya bayan nan da ya kai jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta dake arewa maso yammacin kasar Sin, inda ya ce ya ga kyakkyawan yanayi, da wurare masu kayatarwa a jihar.
Tangara ya kara da cewa, Gambia na matukar goyon bayan manufofin Sin, don gane da batun Taiwan da Xinjiang, kuma za ta ci gaba da nacewa manufar Sin daya tak a duniya. (Saminu Alhassan)