Alkaluman ma’aikatar lura da harkokin sufuri ta kasar Sin sun nuna karuwar tafiye-tafiyen fasinjoji, a ranakun hutun murnar ranar ‘yan kwadago ta duniya a bana, tun daga ranar farko ta bikin wato ranar Alhamis da ta gabata, matakin da ya shaida kara farfadowar bukatun yawon bude ido da karsashin tattalin arziki.
Alkaluman sun nuna cewa, jimillar zirga-zirgar fasinjoji tsakanin yankunan kasar Sin a ranar Alhamis ya karu da kaso 6.2 bisa dari a shekara, inda adadin ya kai miliyan 332.7, kuma kason matafiyan dake bin titunan mota shi ne kan gaba, inda ya karu da kaso 4.7 bisa dari a shekara zuwa zirga-zirga miliyan 305.61.
- Jami’ar Tarayya Ta FUGA Ta Kirkiro Da Injin Kyankyasar ‘Yan Tsaki
- Bayan Fara Binciken $2.96bn, An Samu N80bn A Asusun Tsohon Daraktan Kamfanin NNPCL
Kazalika, adadin fasinjoji da suka yi tafiye-tafiye ta ruwa a ranar ya karu da kaso 87.5 bisa dari idan an kwatanta da rana makamanciyarta a bara, yayin da tafiye-tafiye ta jiragen sama suka karu da kaso 8.9 bisa dari.
A daya bangaren kuma, sashen sufurin jiragen kasa na Sin, ya gudanar da zirga-zirga kusan miliyan 23.12, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari, kamar dai yadda alkaluman kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin suka nuna.
Har ila yau, idan an kwatanta da tafiye-tafiye masu cin gajeren zango da Sinawa suka fi gudanarwa cikin kwanaki 3 na bikin sharar kaburbura na Qingming, an gudanar da zirga-zirga zuwa wurare masu nisa, tare da lekawa wuraren dake kusa da kan iyakokin kasar a ranakun hutun murnar ranar ‘yan kwadago ta duniya a bana.
Wasu alkaluma na daban, daga shafin hidimar tafiye-tafiye na Qunar.com, sun nuna cewa, a ranar Alhamis, adadin wuraren da masu yawon bude ido suka ziyarta a dukkanin sassan kasar Sin ya kai gundumomi 1,229, inda aka samu karuwar odar hidimomi masu nasaba da hakan da kaso 20 bisa dari a shekara. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp