Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce matakan cimma moriyar kashin kai, ba da kariyar cinikayya, da cin zali irin na tattalin arziki da Amurka ke aiwatarwa, ba su takaita ga manyan kasashe masu wadata ba, domin kuwa matakan sun shafi har kananan kasashe masu rauni irin su Haiti.
Geng Shuang, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin zaman tattaunawa na kwamitin tsaron MDD, don gane da yadda Amurka ta kakabawa kasar Haiti harajin kaso 10 bisa dari na hajojinta da ake shigarwa Amurka a matsayin mafi karancin harajin fito, ya ce bisa tarihi Amurka ce ke sarrafa yanayin siyasar Haiti.
- Za A Yi Jana’izar Fafaroma Francis A Ranar Asabar A Vatican
- Sin Na Hasashen Samun Karin Yabanya A Shekarar 2025
Jami’in ya kara da cewa, sama da shekaru 100, Amurka ta mamaye Haiti, ta rika goyon bayan ‘yan kanzaginta dake mulkin kasar, ta tsoma hannu cikin sauya kundin tsarin mulkin kasar, ta kuma yi matukar tasiri a siyasar kasar. Kazalika, kimanin shekara daya da ta gabata, Amurka ta tsoma hannu cikin tsarin mika mulki na kasar Haiti, kafin daga bisani ta yi watsi da hakan biyowa bayan na ta matsalolin siyasar na cikin gida, lamarin da ya haifar da rashin jituwa da hargitsi a kasar ta Haiti.
Daga nan sai Geng Shuang ya bayyana matsayar kasar Sin don gane da hakan, yana mai cewa, kasar na matukar jajantawa al’ummun Haitian bisa halin da suka shiga. Yana mai kira ga daukacin al’ummun duniya da su ci gaba da taimakawa kasar wajen karfafa tsare-tsarenta na ikon gina kai, da rungumar tafarkin neman ‘yancin kai, da dogaro da kai, da gaggauta hawa turbar neman ci gaba na kashin kai. Yayin da hakan ke wakana, Sin za ta ci gaba da taka rawar gani tare da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki na kasar ta Haiti. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp