Kasar Sin ta bayyana adawa da hadin gwiwar soji tsakanin Amurka da yankin Taiwan, haka kuma ba ta amince Amurka ta samar da makamai ga yankin ba, tana mai bukatar Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai na yau Talata.
- Kasar Sin Na Taimakawa Kasashen Afirka Bunkasa Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko
- Ma’aikatan Kamfanin Samar Da Lantarkin Kaduna Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Ya kara da cewa, idan idon Amurka ya rufe da neman danne kasar Sin, to kanta za ta yi wa illa, kuma ba takara ce za ta bayyana ma’anar dangantakar Sin da Amurka ba.
Ya ce, bangaren Sin na bukatar Amurka ta ajiye bambancin dake tsakaninta da Sin, su hada hannu tare wajen inganta raya dangantakar kasashen biyu cikin aminci da karko kuma bisa yanayi mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)