Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Talata cewa, Sin ba ta taba neman rarar cinikayya da kungiyar tarayyar Turai da gangan ba, kuma idan da gaske ne kungiyar EU na son magance wannan batu, to ya kamata ta cire takunkumin hana fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin, maimakon dora laifin a kan kasar Sin.
Takunkumin EU na hana fitar da kayayyakin fasaha na zamani zuwa kasar Sin a cikin ‘yan shekarun nan, kai tsaye ya takaita ikon da kungiyar EU ke da shi na samun damar fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin, lamarin da ya haifar da rashin daidaiton ciniki tsakanin sassan biyu, in ji kakakin.
An ba da rahoton cewa, Brussels za ta matsa wa Beijing lamba don rage shinge a kan kayayyaki da Turai ke fitarwa a wani babban taron da za a yi a watan Satumba. (Mai fassara: Yahaya)