• English
  • Business News
Sunday, October 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: Ba Za A Iya Kare Mata Da Yara Ba, Illa A Tsagaita Bude Wuta Da Kuma Wanzar Da Zaman Lafiya

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce ba za a iya kare mata da kananan yara daga illolin rikicin kasar Ukraine ba, illa a tsagaita buda wuta da kuma maido da zaman lafiya.

Yana mai cewa, bayar da tallafin makamai da sanya takunkumi, ba za su haifar da komai ba, sai tsawaita lokacin rikicin da kuma fadada rikicin zuwa wasu wurare.

Dai Bing ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin da kwamitin sulhu na MDD yake nazari kan batun cin zarafi ta hanyar lalata da kuma fataucin mutane da rikicin kasar Ukraine ya haifar.

Dai Bing ya kara da cewa, rikicin Ukraine ya haifar da dimbin asara ga fararen hula, musamman ma mata da kananan yara, inda suke fuskantar babbar barazanar tsaron lafiyarsu, wanda ke jawo damuwa matuka.

A cewarsa, kamata ya yi bangrorin da rikicin ya shafa su mutunta dokokin kasa da kasa, su dauki matakan kare fararen hula daga kowane irin nuna karfin tuwo, ciki hadda cin zarafin mata da kananan yara mata ta hanyar lalata da kuma fataucinsu.

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

Tun bayan barkewar rikicin, al’ummar Ukraine kimanin miliyan 6 da dubu 800, yawancinsu mata da kananan yara, sun ketare iyakokin kasar, inda suka shiga kasashe makwabta don samun mafaka.
Dai Bing ya ci gaba da cewa, kawar da cin zarafi ta hanyar lalata da kuma fataucin mutane sakamakon barkewar rikici ba za su isa ba. Ya ce ba za a iya kare mata da kanana yara daga illolin rikici ba, sai an tsagaita bude wuta da maido da zaman lafiya.

Ya ce kamata ya yi kasashen duniya su hada hannu wajen kara azama kan ci gaba da yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

Ya ce ana fatan za a warware batun abinci na Ukraine da kuma taimakawa bangarori masu ruwa da tsaki kara amincewa da juna a yayin taron da kasashen Rasha, Ukraine, MDD, da kasar Türkiye za su gudanar nan gaba ba da dadewa ba. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza
Daga Birnin Sin

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

October 11, 2025
Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata
Daga Birnin Sin

Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

October 11, 2025
Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 
Daga Birnin Sin

Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 

October 11, 2025
Next Post
Xi Ya Kai Ziyara Birnin Meishan Dake Kudu Maso Yammacin Kasar Sin

Xi Ya Kai Ziyara Birnin Meishan Dake Kudu Maso Yammacin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

October 11, 2025
Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

October 11, 2025
Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

October 11, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 

Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

October 11, 2025
Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

October 11, 2025
An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

October 11, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.