Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kamata ya yi kasar Amurka ta aiwatar da matakai na hakika, wadanda za su taimakawa kasashe masu tasowa, wajen sa kaimi ga hukumomin hada-hadar kudade na kasa da kasa, da su warware basussuka, maimakon bullo da salon fito-na-fito tsakanin yankuna daban daban.
Wang Wenbin, ya yi wannan tsokaci ne a yau Laraba, yayin taron manema labarai da ya gudana, a matsayin martani ga kalaman sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen.
An dai hakaito Yellen na cewa, hukumomin hada-hadar kudade na kasa da kasa, kamar asusun ba da lamuni na IMF, da bankin duniya, na gudanar da harkokin su ne bisa salo na akidun Amurka. Ta kara da cewa, kasar Sin ba ta cancanci samun rance daga bankin duniya ba. (Saminu Alhassan)