Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasarsa da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya.
Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Juma’a, yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump. Shugaba Xi ya ce domin cimma burikansu, kamata ya yi kasashen biyu su yi azamar aiwatar da hadin gwiwar martaba juna, da zama lami lafiya da juna, da kuma gudanar da hadin gwiwar cimma nasara tare.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci. Kuma tattaunawar baya bayan nan da tawagogin kasashen biyu suka gudanar, ta shaida ruhin daidaito, da martaba juna, da cimma moriya tare. Ya ce ya dace sassan biyu su ci gaba da zantawa kan muhimman batutuwa masu nasaba da dangantakarsu, tare da zage-damtse wajen cimma moriyar bai daya.
Kazalika, shugaban na Sin ya ce ya kamata bangaren Amurka ya kaucewa daukar matakan sanya shingen cinikayya na bangare daya, don magance mayar da hannun agogo baya, kan nasarorin da sassan biyu suka riga suka cimma ta hanyar tattaunawa a mabanbantan lokuta.
Har ila yau, shugaba Xi, ya yi kira ga bangaren Amurka da ya samar da wata budaddiyar kafa ta adalci, wadda ba za ta rika nuna wariya ga kamfanonin Sin masu zuba jari a Amurka ba.
A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Daga nan sai ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin kasarsa da Sin. (Saminu Alhassan)