Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, sun gana a birnin Vientiane na kasar Laos a jiya Asabar, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da alakar sassan biyu, tare da amincewa da wanzar da shawarwari a dukkanin matakai, da zurfafa aiwatar da muhimman matsaya da shugabannin kasashen su suka cimma a watan Nuwamban bara a birnin San Francisco.
A ganawar ta jiya, mista Wang ya ce cikin watanni 3 da suka gabata, jami’an diflomasiyya, da na hada hadar kudade, da na shari’a, da masana batun sauyin yanayi, da sojojin kasashen biyu, sun tattaunawa da juna, baya ga fannin musaya tsakanin al’ummun sassan biyu.
- Wakilin Sin Ya Bukaci A Tsagaita Bude Wuta A Gaza
- Ribar Masana’antun Sin Ta Karu Da Kashi 3.5% A Watanni Shidan Farkon Bana
Sai dai kuma duk da hakan, Wang ya ce ya zama wajibi a lura cewa, har yanzu bangaren Amurka bai dakatar da matakansa na dakilewa, da kokarin danne kasar Sin ba, maimakon samun sauki matakan karuwa ma suke yi.
Ya ce Amurka ta dau matsayar kuskure game da Sin, inda take kallon kasar ta mahangar danniya. A nata bangare kuwa, Sin ba ta bukatar yin babakere, ko shiga siyasar nuna karfin tuwo, kuma a matsayin ta na babbar kasa, Sin na da tarihin zama a sahun gaba a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasashen duniya.
Daga nan sai ministan wajen na Sin ya ce yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin kuma bai taba zama, kuma ba zai taba zama kasa mai cin gashin kai ba. Ya ce kokarin ‘yantar da Taiwan na iya gurgunta yanayin zaman lafiya a zirin Taiwan.
A nasa bangare kuwa, Blinken cewa ya yi Amurka na matukar fatan daidaita alakar ta da Sin, kuma za ta ci gaba da bin manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya. Kaza lika, Amurka na fatan shawo kan bambance bambancen dake tsakanin ta da Sin, tare da kaucewa rashin fahimtar juna da fadawa mummunan tafarki. (Saminu Alhassan)