Wakilan kasar Sin da na Amurka sun yi taro da safiyar yau Asabar don tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata, wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwa game da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, bisa muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin da suka tattauna ta wayar tarho a wannan shekarar.
Mataimakin firaministan kasar Sin kuma memba na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin He Lifeng ne ke jagorantar tawagar kasar ta Sin a tattaunawar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)











