Wakilin kasar Sin a fannin cinikayyar kasa da kasa, wanda kuma shi ne mataimakin ministan cinikayya na kasar, Li Chenggang, ya yi musayar ra’ayoyi da jami’an gwamnatin Amurka, dangane da alakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu.
Li, ya jagoranci tawagar kasar Sin yayin zantawa da jami’an ofishin baitulmalin Amurka, da na ma’aikatar cinikayya, da na ofishin wakilin cinikayyar kasar, tsakanin ranakun Laraba da jiya Jumma’a a birnin Washington.
Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayyar Sin ta fitar bayan ganawar, ta ce sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi dangane da yadda za a aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin zantawarsu ta wayar tarho a ranar biyar ga watan Yunin bana, da ingiza alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu, da kuma bibiyar sauran batutuwan da kasashen biyu suka tattauna, dangane da raya hada-hadar cinikayya tsakaninsu.
Bugu da kari, Li ya jaddada cewa, wajibi ne Sin da Amurka su nacewa ka’idojin mutunta juna, da wanzar da zaman lafiya, da hadin gwiwar cimma moriya tare. Ya ce ya kamata kasashen biyu su yi amfani da salon gudanar da shawarwarin raya tattalin arziki da cinikayyarsu, wajen warware sabani ta hanyar tattaunawa, da tuntubar juna kafada da kafada, su kuma fadada hadin gwiwa, da yin aiki tare don inganta kyakkyawar alakar tattalin arziki da cinikayya mai daidaito da dorewa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp