Domin cimma nasarar aiwatar da matsayar da shugabannin Sin da Amurka suka cimma yayin taron Bali na Indonisiya, da wadanda aka cimma tsakanin mataimakin firaministan Sin, kuma jagoran tawagar raya tattalin arziki da cinikaya na kasar He Lifeng, tare da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, kasashen biyu sun amince su kafa rukunin aiwatar da matakan raya tattalin arzikin su, mai kunshe da rukunin aiwatar da manufofin raya tattalin arziki, da na raya hada hadar kudade.
Rukunnan biyu dai za su rika gudanar da tattaunawa a kai a kai, domin karfafa shawarwari, da musaya a fannoni masu nasaba da raya tattalin arziki, da hada hadar kudade tsakanin kasashen 2. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp