Kasar Sin da hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, sun sake sabunta hadin gwiwarsu, game da bunkasa amfani da fasahohin zamani wajen raya noma, da tsarin samar da abinci mai jure kalubale a sassan nahiyar Afirka.
Da yake tabbatar da hakan a jiya Jumma’a, cikin jawabinsa a taron masu ruwa da tsaki, wanda aka yiwa lakabi da “Haduwar Sin da Afirka”, wanda kuma ya gudana a cibiyar birni ta gwajin fasahohin noma dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, shugaban tawagar Sin a AU Jiang Feng, ya ce hadin gwiwa a fannin raya noma muhimmin bangare ne na cimma moriyar juna tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Ya kuma bayyana cewa, Sin ta kaddamar da cibiyoyin gwajin dabarun bunkasa noma sama da 20, da ingiza cin gajiyar fasahohin zamani na habaka noma sama da 300 a sassan Afirka, matakin da ya amfani kananan manoma sama da miliyan guda.
A nata tsokaci, kwararriya a fannin raya noma, da tabbatar da samar da isasshen abinci a hukumar gudanarwar AU, Patience Mhuriro-Mashapa, ta jinjinawa kwazon kasar Sin na wanzar da hadin kai tare da Afirka, musamman karkashin shirye-shirye da dama na bunkasa sanin makamar aiki.
Ta ce taimakon kasar Sin ga kasashen Afirka, a fannin ingiza zamanantar da harkar noman zamani, ya yi matukar karfafa kwarewar aiki, da bunkasa kwazon cibiyoyi masu nasaba da hakan, kana ya samar da wata babbar kafa ta musayar ilimi a fannin ayyukan gona. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp