Kasar Sin da Tarayyar Afrika (AU), sun yi alkawarin karfafa goyon bayan juna wajen gina tsarin jagorantar harkokin duniya bisa adalci tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya.
An yi alkawarin ne a ranar Juma’a yayin wani taron manyan jami’ai a Addis Ababa na Habasha, albarkacin cika shekaru 80 da Sinawa suka yi nasarar turje wa harin Japan da yakin duniya na II.
Da yake jawabi ga taron, Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a AU, ya nanata bukatar tunawa da tarihi da karfafa hadin gwiwa a duniya domin shawo kan kalubalen tsaro da duniya ke fama da su.
Da yake jawabi a madadin kwamishinar kula da harkokin lafiya da jin kai da ci gaban al’umma Amma Twum-Amoah, babban mai ba ta shawara Pamoussa Zackaria Konsimbo, ya bukaci a kara daidaita tsarin jagorantar duniya, ta yadda zai kasance bisa ka’idojin adalci da martaba cikakken ‘yanci da cudanya tsakanin bangarori daban daban. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp