Kasashen Sin da Brazil da Afrika ta Kudu da Tarayyar Afrika (AU), sun kaddamar da shawarar hadin gwiwar kasa da kasa don baiwa kowa damar cin gajiyar ilimin kimiyya, wadda ake kira da “Open Science International Cooperation Initiative.” Manufar shawarar ita ce, hada hannu wajen gina muhalli mai tabbatar da adalci da bude kofa, ba tare da wariya ba a duniya, domin bunkasa harkokin da suka shafi kimiyya da fasaha, da samar da alfanun kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na duniya ga kasashe masu tasowa.
A yau Alhamis aka fitar da cikakken daftarin wannan shawara a hukumance.
A cewar shawarar, samar da dama mai dorewa ta cin gajiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ga kowa, ta dace da inganta samun ci gaban tattalin arziki mai karfi da dorewa kuma bisa daidaito, tare da gaggauta aiwatar da ajandar MDD ta 2030, wadda ke da alaka da kyautata rayuwar dukkanin bil’adama. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp