A shekarar bana ne ake cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da kungiyar EU, kana ake cika shekaru 80 da kafuwar MDD, a gabar da kuma dangantakar Sin da EU ke shiga wani sabon lokaci a tarihi.
A jiya Alhamis, Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen, wadanda suka zo birnin Beijing domin halartar taro na 25 na Sin da EU, inda kuma shugaba Xi ya gabatar da shawarwari uku, kan makomar raya dangantakar Sin da EU, yana mai jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su girmama juna, da zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu.
- An Amince Da Biranen Kasar Sin 9 A Matsayin Biranen Dausayi Na Kasa Da Kasa
- Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta
Shugaban na Sin ya ce, kamata ya yi sassan biyu su aiwatar da bude kofa ga kasashen waje, da yin hadin gwiwa, da daidaita matsalolin dake tsakaninsu, da rungumar ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da tabbatar da biyayya ga ka’idojin kasa da kasa.
A nasu bangaren kuwa, shugabannin bangaren EU cewa suka yi shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar suna da muhimmanci sosai, sun kuma yi imani, da nuna goyon baya ga kasar Sin da samun karin ci gaba, kana ba su da nufin raba-gari da kasar Sin, kuma kamata ya yi EU da Sin su yi hadin gwiwa don tinkarar kalubalen duniya tare.
Forfesa Wang Yiwei, na sashen nazarin dangantakar kasa da kasa na jami’ar Renmin ta kasar Sin, ya yi tsokaci kan hakan, yana mai cewa, shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, sun zama taswirar manufofin Sin da EU, a fannin mayar da hankali ga hadin gwiwa, da kawar da cikas a tsakaninsu, da kuma yin kokari tare, wajen tinkarar kalubalen duniya baki daya, ta yadda hakan zai samar da kuzari ga raya dangantakar dake tsakanin sassan biyu, bisa kyakkyawar makoma a shekaru 50 masu zuwa, kana zai haifar da moriya ga dukkanin duniya.
Duk da cewa yanayin duniya ya yi babban sauyi, kamata ya yi a mayar da hankali ga hadin gwiwa, yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da EU, kana bangarorin biyu su bi hanya mafi dacewa, da samun kyakkyawar makoma a shekaru 50 masu zuwa, da kuma kara samar da gudummawa ga dukkanin sassan duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp