Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Janhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso, jiya Juma’a a birnin Beijing, inda suka yi alkawarin hada hannu wajen inganta raya dangantakar Sin da Afrika.
Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Janhuriyar Congo, ta zama misalin hadin gwiwa da goyon baya dake tsakanin Sin da Afrika.
Wang Yi ya kuma yi kira ga kasashen Sin da Afrika da su hada kai da kara hadin gwiwa domin kare muradun kasashe masu tasowa, da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a duniya yayin da ake fuskantar hargitsi.
A nasa bangare, Jean-Claude Gakosso, ya ce Janhuriyar Congo na daukar matsayinta na daya daga ci shugabannin dandalin FOCAC da muhimmanci, kuma a shirye take ta hada hannu da kasar Sin wajen shirya taron ministoci masu aiwatar da sakamakon taron FOCAC, da baje kolin cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afrika, da kuma kara samar da sakamako daga hadin gwiwar Sin da Afrika. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp