A yau Alhamis ne kasashen Sin da Kenya suka yanke shawarar daukaka dangantakar dake tsakaninsu zuwa ta gina al’ummar Sin da Kenya mai kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani.
An yanke shawarar ne a yayin tattaunawa tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Kenya William Ruto a nan birnin Beijing. Inda Xi ya ce, daukaka huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa gina al’ummar Sin da Kenya mai kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, zabi ne mai muhimmanci ga bangarorin biyu. Yana mai cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya wajen tinkarar kalubale daban-daban ta hanyar hadin kai, da kiyaye hakki da moriyarsu, da yin riko da ka’idojin cinikayya na kasa da kasa, da kiyaye adalci da daidaici a duniya. Xi ya kuma jaddada cewa, babu wanda zai yi nasara a yake-yaken harajin fito da cinikayya.
A nasa bangare kuwa, Ruto cewa ya yi, yakin cinikayya yana lalata ka’idoji da tsarin kasa da kasa da ake da su, kuma kasar Kenya ta yaba da rawar da kasar Sin ta taka a matsayin mai tabbatar daidaito a halin da ake ciki na rashin daidaito, da kokarin da kasar Sin ke yi na kiyaye hakki da moriyar kasashe masu tasowa a duniya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp