Jakadan kasar Sin dake tarayyar Najeriya Cui Jainchun ya gana da ministan kiwon lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, inda suka sa hannu kan takardar kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin asibitoci na hukumar lafiya ta kasar Sin da ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya.
Sun kuma yi musanyar ra’ayi kan yadda sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangaren kiwon lafiya.
Yayin ganawar da suka yi a Abuja a ranar 19 ga wata, jakada Cui ya bayyana cewa, asibitin al’umma ta jami’ar Peking da asibiti jami’ar Abuja, za su hada gwiwa domin tabbatar da matsayar da aka cimma yayin taron koli na musamman na hadin kan Sin da Afirka domin kandagarkin cutar COVID-19, tare da kara karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a bangaren kiwon lafiya.
Ya ce kasar Sin tana son hada hannu da Najeriya domin hanzarta aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka.
A nasa bangaren, minista Osagie Ehanire ya ce, ya yi farin ciki matuka da ganin an sanya aikin kiwon lafiya a gaba da komai yayin da sassan biyu wato Sin da Afirka suke gudanar da hadin gwiwar a tsakaninsu, yana mai cewa, Najeriya na fatan koyon fasahohin da daga matsayin hadin gwiwarsu, tare kuma da amfanawa al’ummomin kasashen biyu. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)