Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da cewa, kasashen Sin, Rasha da Afirka ta Kudu, za su gudanar da wani atisayen hadin gwiwa a teku a gabar gabashin tekun Durban da Richards Bay na kasar Afirka ta Kudu daga ranar 20 zuwa 27 ga watan Fabrairu.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar Lahadin nan, ta bayyana cewa, atisayen zai taimaka wajen inganta hadin gwiwa a fannin tsaro da na soji a tsakanin kasashe mambobin kungiyar BRICS da kara karfin kasashen uku na kare tsaron teku.
A watan Nuwanban shekarar 2019 ma, kasashen uku sun gudanar da atisayen hadin gwiwa a teku. (Ibrahim)