Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta sanar da yau Lahadi cewa, bisa gayyatar da bangaren kasar Sin ya yi, babban sakataren majalisar tsaro ta tarayyar Rasha, Patrushev Nikolai, zai ziyarci kasar Sin a yau Lahadi da gobe Litinin, don halartar taro na 17 na tattauna batun tsaron Sin da Rasha, gami da taro na 7, na tsarin hadin gwiwa a bangaren aiwatar da doka tsakanin kasashen Sin da Rasha. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp