Dangane da bayanin da ministan kudi na kasar Bangladesh ya yi kan rahotannin karya da kafofin yada labaran Burtaniya suka yi kan kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Litinin din nan cewa, hakan ya nuna irin cikakkiyar amincewa da juna dake tsakanin Sin da Bangladesh, kuma hakan ya tabbatar da abin da kasar Sin ta sha fada cewa, gaskiya ba ta buya, kuma adalci yana bayyana kansa.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, har kullum kasar Sin tana tare da sauran kasashe masu tasowa, kana tana gudanar da hadin gwiwar “ziri daya da hanya daya” bisa tsarin tuntubar juna, da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna. Bayanai sun tabbatar da cewa, batun “tarkon bashi na kasar Sin” a zahiri wani “tarkon tattaunawa ne” da wasu mutane masu mugun nufi suka kirkira, don kawo cikas da kuma gurgunta hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa.
Shawarar ziri daya da hanya daya, ta samu gagarumin goyon baya da shigar da kasashe masu tasowa da dama. Haka kuma hadin gwiwar ta haifar da kyakkyawan sakamako, ta kuma samar da fa’ida ta hakika ga jama’ar dukkan kasashe.
A game da shaidu kuwa, duk wasu kalamai marasa kyau da ke neman bata sunan shawarar da hadin gwiwar Sin da sauran kasashe masu tasowa, zai koma kansu ne.(Ibrahim)