• Leadership Hausa
Thursday, March 23, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taimako Ko Barna?

by Sulaiman Bala Idris
7 months ago
in Rahotonni
0
Taimako Ko Barna?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Idan ka gabatar da wannan maudu’in a matsayin tattaunawa a Nijeriya, musamman a Arewacin Nijeriya zai zama wani bakon abu ne har ma ya zama tasirinshi zai iya razana kwakwale ko kuma ya jefa mutum cikin dogon tunani mai sarkakiya, cakude da shakku a kan anya hakan na aukuwa kuwa?

Ba mutum gudummawa ya halaka kanshi ‘Assisted Suicide’ ya na nufin hadin gwiwa tsakanin wanda ke son ya kashe kanshi da wani mutum domin hakar wanda ke son mutuwan ta cimma ruwa.

  • Wacce Kungiya Za Ta Lashe Firimiyar Ingila?
  • Masarautar Mubi Da Kyakkyawan Shugabancin Sarki Alhaji Abubakar Isa Ahmadu

Abin da a ke nufi da halaka kai bisa zabin rai ‘suicide’ shi ne mutum ya yi sanadin mutuwar kanshi da kanshi.

Akwai bambanci tsakanin mutum ya halaka kanshi bisa zabi ‘suicide’ da kuma kisan da sai an bashi gudummawa wurin halaka kanshi din ‘Assisted suicide’.

Neman tallafin wani domin mutum ya halaka kanshi ya na aukuwa ne a mafi yawancin lokuta yayin da wata cuta wacce ta ki ci ta ki cinyewa ta addabe shi.

Labarai Masu Nasaba

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 

Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya

Idan har mutum ya na sane ya ba wani gudummawa ko da da shawara ce, wacce ta yi sanadiyyan halakarshi a doka su biyun ne ke da alhakin kisan.

An fi samun irin wannan a asibiti, inda likitoci kan ba marasa lafiya magunguna ko allurar da za ta katse masu rayuwa.

Duk da ba a asibiti kadai a ke aikata irin wannan ba, amma a can din a ka fi yin haka.

Marasa lafiya da ke fama da miyagun cututtuka, su kan cire tsammanin cewa likitoci za su iya taka wata muhimmiyar rawa ga samuwar lafiyarsu, da irin wannan tunanin ne su ke hana likitoci su gabatar da aikin da ya dace akansu.

A na iya ganin haka yawanci ga masu cututtukan kansa, da nakasan wani muhimmin bangare na jikin dan Adam.

Da yawan marasa lafiyan da kan nemi gudummawar likitoci don a katse rayuwarsu su na yin haka ne saboda matsanancin radadin cutar da ke addabarsu, ba tare da yin la’akari da rashin tabbas na abin da za su je can su taras ba.

A wani bangare na nazarin kuma, akwai wadanda ke kashe mai jinya bisa dalilin wai su na tausayin wannan mara lafiyan a kan wahalhalu da azaban ciwo da ya ke fama da su.

Likitoci na yin irin wannan a wasu lokutan ta hanyar yin allura.

A na kiran irin wannan kisa da ‘Euthanasia’.

Mafi yawa irin wannan, dangin mara lafiyan ne su ke gabatarwa da likitocin da bukatar a katse a rayuwar majinyacinsu, saboda ya na wahalar da su, kuma ciwon babu alamar samun sauki.

Hatta a tsakankanin masana tun a }arnonin baya akwai taraddadi da shakka kan ra’ayin kisa don tausayi, don wahalar rayuwa ko kuma don radadin ciwo.

Ko kadan a lokutan baya ba a yi sakacin aminta da wannan muguwar dabi’a ba, sai a ‘yan kwanakin nan ne ma a ke tattauna batun don ganin ko zai yiwu a halasta shi ko a haramta.

A tsakankanin shekarar 1970 ne a ka kaddamar da dokar da ke halastawa mara lafiya bijirewa kin aikin likitoci ga cutarshi, wanda kafin nan ko da mutum bai so sai an yi mai aiki matukar ya na fama da ciwo.

Daga wannan ne kuma a ka samu bayyanar ra’ayin neman gudummawa don halaka kai, da kuma halaka mai ciwo don tsananin tausayin halin da ya ke ciki.

Wasu na ganin ya kamata a kaddamar da dokar halascin bayar da gudummawa ga mutum ya kashe kanshi, domin da hakan ne a cewarsu kowa zai samu damar tsara yanayin irin mutuwar da ya ke so.

Wannan ra’ayi bai zo ya samu wuri ya zauna ba, akwai zazzafan martani daga wasu masanan a kan masu yekuwar a halasta dokar, sun ce halasta wannan aiki zai jawo yawaitar alfasha da danyen aiki. Idan a ka ce haka, lallai talauci, rashin aikin yi da kuma fargabar wani abu zai yi ta sa mutane su na neman gudummawar kashe kawunansu.

A ta fannin addini kuwa, masana a ilmin sanin halayyar jama’a da zamantakewa sun tabbatar da illolin wannan aiki, har ma su ka ce mutuwa da rayuwa al’amari ne na Allah, duk wanda ya kashe kanshi saboda wani tsanani ya yi mummunan karshe ne, kuma makomarshi sai ta fi tsananta fiye da tsananin da ya bari a duniya.

Wani shahararren likita da ke zaune a Michigan mai suna Keborkian a tsakankanin 1990 ya yi ta ba marasa lafiya gudummawa su na mutuwa.

Likita Keborkian ya gudanar da wannan aika – aika ne da ta hanyar amfani da wata na’ura mai guba, wacce a ke yiwa lakabi da ‘Death Machine’, akwai wacce ya shirya da zaran mara lafiya ya latsa ta zai halaka.

A Turai ma an yi dirar mikiya a kan likita Keborkian, har ma wasu lauyoyi da ‘yan rajin kare hakkin bil’adama sun yi maka shi a kotu mabambanta, amma alkalai su na kawo tsaiko ga sauraron shari’arshi.

Sai a shekarar 1999 ne wani alkali ya yanke mai hukuncin shekaru 10 zuwa 20 a gidan kurkuku. Haka nan su ma likitoci ‘yan uwan Keborkian sun yi Allah wadai da irin aikinshi.

A Nijeriya ma akwai irin wannan kwamacalar da sunan taimako, musamman ma a jihohin Kudanci.

Wani sashe na Kudancin su na kashe ‘ya ‘ya ne wadanda a ka haifa da cutar Kuturta da ma wasu dangi na nakasar jiki.

A Arewacin Nijeriya ma a na yi, za ka iya tunanin ba haka ba ne, amma kuma hakan ne. A yanzun yankin ya cika ya batse da asibitocin biyuu-ahuu wadanda likitoci ke cin karensu ba babbaka wurin zubar da ciki.

Dubban cikin da likitoci ke zubarwa shi ma gudummawa ce su ke ba wacce (macen) ta ke dauke da cikin da kuma wanda (namijin) ke da alhakin cikin wurin halaka jinjirin da bai ji ba bai gani ba. Idan kin san ba ki so, ko kuma ka san ba ka so, me ya kai ku aikatawa? Mu hadu mako mai zuwa!

Tags: CiwoKimiyyar ZamantakewaLikitociRadadiWahala
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin: Gaskiya Ba Ta Buya, Kuma Adalci Yana Bayyana Kansa

Next Post

Miyetti Allah Ta Maka Gwamna Ortom A Kotu Kan Kwace Wuraren Yin Kiwo A Jihar Benuwai

Related

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 
Rahotonni

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 

1 week ago
Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya
Rahotonni

Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya

2 weeks ago
Sin Ta Taya Murnar Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Nijeriya
Rahotonni

An Fara Zawarcin Mukaman Siyasa A Gwamnatin Tinubu

2 weeks ago
Zaben Gwamnoni: Jihohin Da Za A Fafata Mai Tsanani
Rahotonni

Zaben Gwamnoni: Jihohin Da Za A Fafata Mai Tsanani

2 weeks ago
‘Yansanda Sun Cafke Mutum 50 Kan Satar Kaya Lokacin Da Gobara Ke Cin Kasuwar Monday Market A Borno
Rahotonni

Waiwaye: Konewar Babbar Kasuwar Maiduguri A Shekarar 1979 Da Sake Gina Ta Da Aka Yi A 1983

3 weeks ago
Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Daga Kananan Hukumomin Jihar Bauchi 
Rahotonni

Manyan Abubuwa Takwas Da Suka Girgiza Zaben Shugaban Kasa Na 2023

3 weeks ago
Next Post
Miyetti Allah Ta Maka Gwamna Ortom A Kotu Kan Kwace Wuraren Yin Kiwo A Jihar Benuwai

Miyetti Allah Ta Maka Gwamna Ortom A Kotu Kan Kwace Wuraren Yin Kiwo A Jihar Benuwai

LABARAI MASU NASABA

Matawalle Ya Karbi Faduwa, Ya Yi Fatan Alheri Ga Sabon Gwamnan Zamfara

Matawalle Ya Karbi Faduwa, Ya Yi Fatan Alheri Ga Sabon Gwamnan Zamfara

March 23, 2023
Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

March 23, 2023
Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

March 23, 2023
Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

March 23, 2023
Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

March 23, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

March 23, 2023
Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

March 23, 2023
NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya

NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya

March 23, 2023
FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA

FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA

March 23, 2023
Mata Magoya Bayan PDP Na Zanga-Zangar Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Kaduna

Mata Magoya Bayan PDP Na Zanga-Zangar Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Kaduna

March 23, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.