A yau Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya sanar da cewa, idan har Amurka da gaske take tana son warware takaddamar cinikayya dake tsakaninta da Sin, ta hanyar tattaunawa da shawarwari, ya zama wajibi ta dakatar da aiwatar da matakan matsin lamba da gangaci.
Lin Jian, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa tambayar da wani dan jarida ya yi masa kan batun, inda ya ce, Sin ta riga ta sha fayyace matsayinta kan batun kare-karen harajin, cewa ba wanda zai yi nasara a yakin cinikayya ko na haraji. Kuma Sin ba ta son tsunduma cikin wannan yaki, amma kuma ba ta tsoron shiga a fafata da ita idan ya tabbata.
Ya ce, duk wata tattaunawa, dole ta wakana bisa tsarin mutunta juna, da girmama juna, da cimma moriya tare, amma idan Amurka ta dage wajen kara ingiza yakin haraji da na cinikayya, to Sin a shirye take ta tunkari kalubalen har zuwa karshe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp