Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya ce kasashe membobin kungiyar G7, suna kira ga kasar Sin da ta bi ka’idojin kasa da kasa, amma kuma a nasu bangare suna wakiltar sabawa ka’idojin kasa da kasa.
Wang Wenbin yi wannan tsokaci ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Alhamis, inda ya ce yawancin kasashen duniya sun amince da ka’idojin raya dangantaka tsakanin kasa da kasa, bisa tushen kundin tsarin mulkin MDD da ka’idojin MDD, wadanda su ne ka’idojin kasa da kasa da ya kamata a bi. Sai dai kasashen G7 ba su ambato kundin tsarin mulkin MDD ba, maimakon haka su kan ambaci ka’idojin kasa da kasa bisa tushen ka’idojin “kasashen demokuradiyya”, wato ka’idojin kasashen yammacin duniya, ko kuma ka’idojin kasashen G7 karkashin jagorancin Amurka.
Wang Wenbin ya kara da cewa, Sin ta kalubalanci kasashen G7 ciki har da Amurka, da Japan, da su biya kudin kasancewa membobin MDD da ba su biya ba cikin shekaru da dama da suka gabata, su kuma janye sojojin su daga kasar Syria, su dakatar da shirin gurbata ruwan teku da sinadaran nukiliya. Kaza lika su kauracewa tada rikici, da nuna kiyayya ga sauran sassa, da kuma dakatar da neman moriyarsu, ta tabbatar da manufar kama karya, su tabbatar da ka’idojin kasa da kasa. (Zainab)