Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Game da taron shigo da jarin waje daga dukkan sana’o’i a tashar ciniki maras shinge ta lardin Hainan na Sin da aka gudanar, Lin ya ce, Sin kasuwa ce ta duniya, kuma dama ce ga kasa da kasa. Yayin da ake fuskantar rashin tabbaci daga waje, Sin za ta tsaya tsayin daka kan ba da tabbaci da kuzari ga tattalin arzikin duniya ta hanyar ci gaba mai inganci da bude kofa mai babban mataki.
Game da batun neman kama Amurkawa ‘yan leken sirri guda uku da ‘yan sandan Sin ke yi, Lin Jian ya ce, bangaren Sin ya yi Allah wadai da munanan ayyukan da gwamnatin Amurka ta yi a kan yanar gizo, kuma za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace don kare tsaron intanet dinta. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp