Jiya Alhamis, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin He Yadong ya furta cewa, yadda kasar Amurka ta kayyade fitar da na’urorin laturoni da wasu fasahohin zamani ba zai hana bunkasuwar kasar Sin ba, sai ma su sa kamfanonin kasar Amurka su fita daga kasuwannin kasar Sin, lamarin da zai haddasa illa ga moriyar kasar Amurka ita kanta. Kuma, kasar Sin za ta mai da hankali sosai kan yanayi da tasirin matakan da Amurka ke dauka, tare da tabbatar da kiyaye moriyarta.
A kwanan nan, sakatariyar harkokin kasuwancin kasar Amurka Gina Raimondo ta yi kira da a hana kasar Sin amfani da na’urorin laturoni da wasu fasahohin zamani, sa’an nan ta ce, daga shekara mai zuwa Amurka za ta kayyade kamfanonin kasar Sin da masu samar da batir samun tallafin haraji kan harkokin dake shafar motoci masu amfani da wutar lantarki.
Game da kalaman Raimondo, He Yadong ya bayyana a yayin taron manema labarai da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta kira, cewar shugabannin kasashen Sin da Amurka sun yarda da daidaita wasu abubuwa na takara a tsakaninsu yadda ya kamata, kuma Sin na fatan hukumomin kasar Amurka da abin ya shafa, za su yi hadin gwiwa da kasar Sin, wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashe biyu suka cimma, a yayin ganawar su a birnin San Francisco na kasar Amurka a kwanakin baya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)